TAKAITACCEN TARAIHIN TASKAR SULTAN MEDIA SERVICES.

Taskar Sultan wata kafa ce da aka kirkire ta domin ta fadakar, ta ilmantar, ta kuma nishadantar cikin sauki. 

Taskar Sultan kafa ce da take gabatar da shirye-shiryen a kafofin sada zumunta na: Facebook, WhatsApp, Instagram, YouTube da kuma Twitter. 

An kirkiri wannan tashar ne a ranar 10 ga watan 3 shekara 2021. Da nufin amfanar da al'umma, ta hanyar kawo musu shirye-shirye masu dadi, da kuma wayar da kai. 

Taskar Sultan tana a garin Potiskum dake jihar Yobe Nigeria. Babban buri wannan tasha shine kawo nesa kusa, ta hanyar gabatar da sahihan labarai,  musammam ga masu sauraron ta. 

Wannan tasha mai suna Taskar Sultan tana gabatar da shirye-shirye a ranaku kamar haka a cikin sati:
1.Ranar Lahdi;
* Sana'o'i da kasuwanci. 
* Tarbiyar iyali. 
* Zaman tare. 
* Ilimi hasken rayuwa. 

2. Ranar Litinin;
* Labaran mako. 
* Waiwaye adon tafiya. 

3. Ranar Laraba;
* Lafiya jari. 
* Tarihin shahidan mu. 
* Labaran wasanni. 
* Kunne abin sauraro. 

4. Ranar Jumu'a;
* Sada zumunci. 
* Shrhin jaridu. 
* Wasa kwakwalwa. 
* Darasi a rayuwar mu. 

5. Ranar Asabat;
* Bakon mu na mako. 
* Duniya labari. 

Lokacin gabatar da shirye-shirye: karfe takwas da rabi na dare, (8:30pm). 

Popular posts from this blog

Da sunan Allah mai rahama mai jinkai, tsira da Amincin Alllah su tabbata ga Annabi da iyalan gidansa tsarkaka, yan uwa barka zuwa *TASKAR SULTAN* wanda duk mako zai na kawo muku shirye-shirye masu nishadantarwa da ilmantarwa.

Da sunan Allah mai rahama mai jinkai, tsira da Amincin Alllah su tabbata ga Annabi da iyalan gidansa tsarkaka, yan uwa barka zuwa *TASKAR SULTAN* wanda duk mako zai na kawo muku shirye-shirye masu nishadantarwa da ilmantarwa.

MATASAN ADAKAWA GROUP SUN GUDANR DA MAULIDI FIYAYYEN HALITTA AGARIN POTISKUN.